Taliban ta kai hare-hare a Afghanistan | Labarai | DW | 01.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taliban ta kai hare-hare a Afghanistan

Taliban ta dauki alhakin kai hare-hare kunar bakin wake a Afghanistan wadanda suka janyo mutuwar kusan mutane 40 tare da jikkata wasu da dama.

Mutane 37 gabilin 'yan sanda yayin da wasu kimanin 40 sun samu raunuka lokacin da kungiyar Taliban ta Afghanistan ta kai hare-hare kunar bakin wake biyu a ranar Alhamis din da ta gabata. An dai kai hare-haren ne kan tawogar motocin 'yan sanda a yammacin birnin Kabul fadar gwamnatin kasar.

A cikin wani sako ga kamfanin dillancin labaran AP, mai magana da yawun kungiyar ta Taliban ya ce su ne suka kai hare-hare. Tsagerun kungiyar Taliban suna kara kaimin kai hare-hare a cikin kasar ta Afghanistan inda zaman lafiya ke tangal-tangal.