1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takunkumi a kan shugabannin Madagaska

June 26, 2013

Ana ci gaba da tirka-tirka a siyasar kasar Madagaska, inda tsofaffin shugabannin kasar da ma shugaba mai ci yanzu ke hana ruwa gudu wajen gudanar da zabe.

https://p.dw.com/p/18x8M
Hoto: AP

Al'ummomin kasa da kasa sun bukaci da a kakabawa shugabannin kasar Madagaska tare da 'yan takara uku da ake zargin sun hana ruwa gudu a zaben shugaban kasa da ake shirin gudanarwa a kasar.

Kungiyar tuntuba ta kasa da kasa GIC ce ta bukaci hakan bayan taron da suka gudanar a shalkwatar kungiyar Tarayyar Afirka dake Adis Ababa babban birnin kasar Habasha domin tattauna batun rikicin siyasar kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan takarar uku da suka hana ruwa gudu a zaben sune shugaban kasar mai ci yanzu Andry Rajoelina, da ya kwaci mulki a hannun Marc Ravalomanana a shekara ta 2009 da uwargidan tsohon shugaban kasar da ta bayyana aniyarta ta tsayawa takara wato Lalao Ravalomanana, sai kuma tsohon shugaban kasar Ratsiraka wanda Ravalomananan ya yi wa juyin mulki.

Kungiyar ta tuntuba ta kasa da kasa, wato GIC ta kuma bukaci da a gaggauta shirya gudanar da sabon zabe a kasar ta Madagaska.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman