Takun saka tsakanin anti-Balaka da Tarayyar Afirka | Labarai | DW | 26.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takun saka tsakanin anti-Balaka da Tarayyar Afirka

Dakarun kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka sun bayyana mayakan anti-Balaka a matsayin makiya

Shugaban dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka da ke kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya bayyana cewa dakarun za su dauki 'yan kungiyar anti-Balaka a matsayin makiya.

Jagoran dakarun Janar Jean-Marie Makoko dan kasar Kwango, ya fadi haka bayan tashin hankalin da ya kai ga mutuwar kimanin mutane 20, sannan aka bude wuta kan dakarun kiyaye zaman lafiya. Sojojin Faransa da dakarun daga Afirka sun bude wuta a karshen mako domin kwantar da wutar rikici, abin da ya janyo mutuwar 'yan anti-Balaka takwas da suka hada da daya daga cikin shugabannin kungiyar.

A wannan Laraba kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta bayyana cewa mutane 16 sun mutu lokacin da 'yan anti-Balaka suka nuna turjiya na mika makamai wa dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen Afirka. Tashe-tashen hankulan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya suna zuwa yayin da wannan mako ake cika shekara guda da kawar da Shugaba Francois Bozize daga kan madafun iko, inda Michel Djotodia ya zama Musulmi na farko da ya shugabancin kasar ta galibi Kiristoci. Amma an tilasta wa Djotodia ajiye aiki a wannan shekara saboda kasa iya magance matsalolin da kasar ta fada a ciki.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar