Takun saƙar Uganda da ′yan janjawid | Labarai | DW | 15.06.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takun saƙar Uganda da 'yan janjawid

ƙasar Uganda ta zargin 'yan janjawid na Sudan da kashe-kashen ba gaira.

default

Sojojin Uganda

Ƙasar Uganda ta zargi sojojin sa kai na Sudan da murƙushe mata sojoji ba tare da wani ƙwaƙwaran dalili ba. Cikin wata hira da yayi da jaridar New Vision a birnin kampala, hapsan hapsoshin sojojin Uganda, wato janar Aronda Nyakairima ya ce 'yan janjawid sun kashe sojojinsu 10 a jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Ƙungiyar 'yan tawaye ta LRA ce gwamantin Uganda ta fara zargi da wannan aika-aika kafin daga bisani ta ƙaryarta labarin. Dama dakarun na Uganda na far ma 'yan awaren na LRA ne a maɓuyarsu da ke jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: umaru Aliyu