TAKADDAMA KANN AMFANI DA KOGIN NIL. | Siyasa | DW | 16.01.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

TAKADDAMA KANN AMFANI DA KOGIN NIL.

Yarjejenniyar shekaru 75 da aka cimma ta yadda da cin moriyar kogin nil a tsakanin kasashe goma da sukayi iyaka dashi na neman shiga wani hali na kaka nikayi,sakamakon barazana da wasu kasashe daga gabashin nahiyar Africa sukayi na ballewa daga wannan yarjejeniya. Ita dai wannan yarjejeniya an dai daita a kann ta ne a shekara ta 1929,a tsakanin kasashen Masar da Sudan da Eritrea da Kenya da Tanzania da Uganda da Rwanda da Burundi da kuma congo.

Kasar Biritaniya a wancan lokaci itace ta wakilci kasashen da tayiwa mulkin mallaka na rattaba hannu kann wannan yarjejeniya na yarda da cewa kasashen ba zasu gudanar da wani aiki ba da zai hana ruwan kogin na Nil isowa izuwa ragowar kasashen ba,musanmamma kasar Masar da kuma Sudan.

A hannu daya kuma bisa rahotannin da suka iso mana dangane da barazanar janyewa daga wannan yarjejeniya da wasu kasashen na gabashin nahiyar ta Africa sukace zasuyi nada nasaba ne da irin rashin adalci da ake nuna musu dangane da yadda ake rarraba ruwan izuwa kasashen dajke cikin inuwar yarjejeniyar amfani dashi ta shekara ta 1929.

Wadan nan kasashe na gabashin nahiyar ta Africa bisa rahotanni sun nunar da cewa wannan yarjejeniya ba wanda yake amfana da ita illa yan mulkin mallaka dake kasashen masar a zaune,domin kuwa bisa yarjejeniyar dole ne idan kasashe irin su Tanzania da Kenya da Uganda zasu janyo ruwa daga kogin Victoria daya hade dana kogin Nil sai sun nemi izini daga mahukuntan na masar kafin zartar da wannan aniya. Hakan a yanzu ya sanya dole kasar kenya na sayo kayan amfanin gona daga kasar ta Masar,musanmamma kayan marmari.

Wanda a don haka daya daga cikin yan majalisar kasar ta Kenya mai suna Paul muite yayi tambayar shin menene dalilin da yasa kasar su ba zata dinga amfani da ruwan na Victoria ko kuma na nil ba wajen shuka ire iren wadan nan kayan marmari. Bugu da kari suma yam majalisar kasar Uganda sun gudanar da irin wannan shawara ta ficewa daga cikin wannan yarjejeniya,domin suna ganin cewa kasashe irin su Sudan da Masar naci da gumin su wajen amfani da ruwan na kogin nil.

Ita kuwa kasar Tanzania da,a yanzu haka mutanen ta ke fama da matsananciyar yunwa ya haifar yan majalisar kasar sun fara musayar miyau dangane da janyewa daga waqnnan yarjejeniya don samun damar amfanar ruwan na kogin Nil yadda ya kamata. A wata sabuwa kuma,kasar Habasha na daya daga cikin kasashen dake bada gudunmawar yawan ruwan na Kogin nil da yawan sa ya kai kashi 86 daga cikin dari amma kuma sai ya kasance bata amfani dako da kashi daya bisa dari na ruwan ta hanyar sarrafashi don yin wasu aiyukan. Bugu da kari ministan ciniki da masana,antu na kasar ta Habasha ya taba sukar lamirin kasar Masar a watan agusta daya gabata da yin kisisinar hana wasu kasashe na duniya daina taimakawa kasar ta basu dabaru irin na zamani na yadda zasu sarrafa ruwan don amfanin kansu. Haka kuma ministan ya tabbatar da cewa kasar ta Masar tayi uwa tayi makarbiya wajen hana kasashen larabawa bawa kasar ta Habasha rancen kudi don habaka noman ruwan na kogin nil.

To amma kuma a hannu daya a lokacin da ministan harkokin waje na masar Fayaza aboulnaga ya kai wata ziyara izuwa Habasha a watan daya gabata yace kasar sa a shirye take ta taimakawa kasar ta Habasha farfado da noman rani a kasar,to amma fa hakan a cewar ministan zai samu ne kawai idan kasar ta Habasha ta nuna kulawa tare da samar da wasu abubuwan da ake nema don gudanar da wannan aiki. To koma dai mai zai faru dangane da wannan takaddama,hausawa dai kance ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare.
 • Kwanan wata 16.01.2004
 • Mawallafi Ibrahim sani.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvmW
 • Kwanan wata 16.01.2004
 • Mawallafi Ibrahim sani.
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/BvmW