Takaddama kan wanda suka kashe Nemtsov | Labarai | DW | 09.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Takaddama kan wanda suka kashe Nemtsov

Magoya bayan madugun 'yan adawar Rasha Boris Nemtsov da aka hallaka a watan jiya sun yi watsi da batun alakar kisansa da aiki irin na masu tsaurin kishin addinin Islama.

Ilya Yashin dan siyasa kana mai fafutuka ta kare hakkin dan Adam a kasar ta Rasha ya ce ko kusa wannan zance abu ne da hankali ba zai dauka ba, inda ya kara da cewar wanda suka sa aka yi kisan ne ke kokarin fakewa da hakan don gujewa laifin da suka aikata.

Mahukuntan Rasha dai sun kame mutane 5 da ake zargi da hannu a kisan na marigayi Nemtsov, kuma galibinsu 'yan yankin Chechnya ne ciki kuwa har da Zaur Dadaev da shugaban yankin Ramzan Kadyrov ya ce mutum ne da kowa ya sani a matsayin mai kaifin kishin addini.