Takaddama kan tafiya aikin Hajji
September 10, 2013A daidai lokacin da ya rage 'yan kwanaki kalilan a soma jigilar
maniyatan kasar ta Nijar zuwa kasar Saudiyya domin sauke faralin
bana kamfanonin Hajji da Umrah na kasar sun koka dangane da
wani mataki da gwamnati ta dauka na karbar wasu kudade sama da
jikka dari na CFA ga kowane maniyaci domin abinci a wurin
kwaciya.
Wanann ya zo ne kwana daya bayan da wasu kungiyoyi suka yi zargin cin hanci wajan bayar da kwangilar jigilar maniyatan da kuma tsauwala farashin kudin jirgi.
To sai dai a wani taron manema labarai da ta kira a ranar Talata hukumar koli mai kula da aikin Hajji da Umrah a kasar ta Nijar wato COHO ta mayar da martani a kan wadannan zarge-zarge da ake yi mata.
Shirye-shiryen fara jigilar maniyata
Da ya ke jawabi a gaban manema labarai shugaban hukumar ta COHO Alhaji Bello Garba ya ce ya zuwa yanzu shirye-shiryen jigilar maniyatan komi na tafiya daidai musamman dangane da batun bisa, sun cimma wani shiri da hukumomin Saudiyya inda kowa zai samu tashi bisar ba tare da wahala ba. Kana kuma kudin kujera zai tashi jikka 950 sabanin 980 a bara. Ya kara da cewa jirgin farko zai tashi ne ranar 15 ga wanann wata na Satumba.
A baya dai wasu kungiyoyin farar hula sun zargi hukumar da
cewa ta hada baki da kamfanin Max Air na Dahiru Mangal domin
kwace kason kujerun wasu kamfanonin da suka samu izinin jigilar
maniyatan kasar da ma daga farashin
kujerar daga jikka 905 da aka cimma a baya zuwa 950.
Sai dai ko baya ga wadannan korafe-korafe lokacin wani taron
manema labarai da suka kira a ranar Talata, kawancan kamfanonin
Hajji da Umrah na BAB Makka sun nuna damuwarsu da wani mataki
da hukumar ta dauka na karbar wasu kudade sama da jikka dari ga
maniyatan da sunan abinci da gurin kwanciya.
Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa
Edita: Mohammad Nasiru Awal