1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama kan sakamakon zaben kasar Angola

Mohammad Nasiru Awal
August 25, 2017

A wannan Juma'ar an tabbatar da nasarar lashe zaben gama gari da jam'iyyar MPLA mai jan ragamar mulki a kasar Angola ta samu, duk da korafe-korafe da kuma fushi da jam'iyyun adawa suka yi cewa an tabka magudi a zaben.

https://p.dw.com/p/2ird1
Angola Wahlen Stimmenauszählung
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Masu sanya ido a zaben na Angola sun goyi bayan sahihancin sakamakon zaben da aka gudanar a ranar Laraba da zai kawo karshen mulkin shekaru 38 da na Shugaba Jose Eduardo dos Santos. 

Angola Alcides Sakala, Sprecher der Partei UNITAs
Alcides Sakala, kakakin jam'iyyar UNITAHoto: DW/J. Carlos

Yanzu haka dai Joao Lourenco da ke zama dan takarar jam'iyyar People's Movement for the Liberation of Angola wato MPLA kuma tsohon ministan tsaro ya kama hanyar maye gurbin shugaban kasa Jose Eduardo dos Santos a mukamin jagoran kasar ta Angola mai arzikin man fetir. Sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar ya nuna cewa jam'iyyar MPLA wadda ke jan ragamar mulkin Angola tun bayan samun 'yancin kanta daga kasar Portugal a shekarar 1975, ta samu kashi 61.1 cikin 100, bayan kammala kidayar kashi 98 cikin 100 na kuri'un da aka kada a babban zaben. Su kuwa manyan jam'iyyun adawa biyu a kasar wato UNITA ta samu kashi 26.7 cikin 100 yayin da Casa-CE ta tashi da kashi 9.4 cikin 100.

Sai dai tuni jam'iyyun adawar sun yi zargin tabka magudi a zaben. Jose Pedro Cachiungo na babbar jam'iyyar adawa ta UNITA ya ce jam'iyyarsa ta tattara cikakkun bayanai da ke tabbatar da cewa akwai kurakurai a sakamakon farko da aka bayar.

Angola Präsidentschaftswahlen Abel Chivukuvuku
Jami'an sa ido na kasashen duniya a AngolaHoto: picture-alliance/Zuma/L. Fernando

Amma fa masu sa ido a zabe na kasa da kasa sun yaba da yadda zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana a kasar ta Angola, suna masu danganta nasarar zaben da irin na mijin aikin da hukumar zaben kasar ta yi. A taron da suka yi da manema labarai wakilan jami'an sa ido su kimanin 1200 da suka shaida yadda zaben ya gudana gaba dayansu sun ce komaim ya tafi salin alim kana masu zabe sun damar sauke wannan nauyi ba tursasawa ko wata tsangwama ba. Bisa sakamakon da aka fitar yanzu MPLA ta samu kujeru 150 daga cikin 220 na majalisar dokoki, adadin da zai ba ta rinjayen kashi biyu bisa uku da take bukata na kafa doka ba tare da neman goyon bayan wata jam'iiya ba.