Takaddama kan hurumin karbar haraji | Siyasa | DW | 28.09.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Takaddama kan hurumin karbar haraji

A Nijar wata takaddama ce ta kunno kai tsakanin gwamnatin kasar da kungiyoyin manyan 'yan kasuwa masu shigo da kaya daga waje da ake zargi da laifin ha’intar gwamnati.

A Jamhuriyar Nijar wata takaddama ce ta kunno kai tsakanin gwamnatin kasar da kungiyoyin manyan 'yan kasuwa masu shigo da kaya daga waje, kan batun wata sabuwar dokar tsarin kasuwanci da gwamnatin ta fito da ita, wacce ke da burin shawo kan matsalar ha’intar gwamnati da wasu manyan 'yan kasuwa ko kamfanoni ke yi hadin baki da wasu jami’an gwamnati wajen kin biyan haraji TVA ko VAT ko karkatar da akalarsa. 

 Sabuwar dokar tsarin kasuwancin wacce aka fi sani da ''Facture Certifiee'' na da burin bibiyar salsalar harkokin kasuwancin duk wani kamfani ko dan kasuwa tun daga kasa da ma kamfanin da ya yo odar hajar tasa, da kudaden da ya kashe har zuwan kayan gida, da ma farashin da yake sayar da kayan nasa da ribar da yake samu a ciki da ma yawan kudaden harajin TVA ko VAT da kamfanin ko dan kasuwan ya karba daga hannun kwastomomi a cikin kowane cinikin.

Westafrika CFA-Franc BEAC

Zargin 'yan kasuwa da kaucewa biyan haraji

Hakan zai bai wa gwamnatin damar karbar daga hannun 'yan kasuwan illahirin kudadenta na harajin TVA da ke zama kaso 19 daga cikin dari na kudin kowace haja da kwastoma ya saya, ba tare da dan kasuwan ya iya ha’intar gwamnatin ba kamar dai yadda ministan kudi na Nijar Ahmed Jidoud ya yi karin bayani.

''Ya ce, harajin TVA haraji mai muhimmanci a tsarin samar da kudaden shiga a cikin kasa, wanda kwastomomi ne masu saye domin amfani ke biyansa wanda kuma da shi ne ake gina hanyoyi da asibitoci da makarantu da tabbatar da tsaro da ma samar da duk wasu ababe na more rayuwa. Amma abin asha, shi ne tsarin da muke amfani da shi shekaru da dama na cike da rauni inda aka wayi gari kwastomomi na biyan harajin amma wasu na amafani da wasu dubaru suna karkatar da akalarsa.“.

Karin Bayani:Nijar: Shirin yaki da cin-hanci da rashawa

Yanzu haka dai bincike ya nunar da cewa kaso 30 cikin dari ne kawai haraji ke samarwa ga kudaden shiga ga gwamnatin Nijar a yayin da a kasashe da dama yake samar da sama da kaso 50 cikin dari. To sai dai sabon shirin kasuwancin ya tanadi dora wata manhajar bin diddigin harkokin cinikayya a kamfutocin kowane dan kasuwa ko kamfani mai rijista a Nijar. Kuma duk dan kasuwan da bai cika wannan ka’ida ba, ba zai sake samun wata kwagila ba. To amma kungiyoyin 'yan kasuwa na kasar ta Nijar na ganin akwai kwara a cikin wannan tsari. Yanzu dai 'yan kasa sun zura ido su ga yadda wannan takaddama za ta kaya tsakanin gwamnati da kuma 'yan kasuwan.

Sauti da bidiyo akan labarin