1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin lafta wa Rasha karin takunkumai

May 9, 2023

Tarayyar Turai na shirin lafta wa Rasha karin takunkumai saboda mamayar Ukraine a yayin da Rashan ke cewa ba makawa har sai ta ga bayan makwabciyarta.

https://p.dw.com/p/4R4eL
Ursula von der Leyen da Volodymyr Zelenskyy
Ursula von der Leyen da Volodymyr ZelenskyyHoto: Virginia Mayo/AP

Shugabar Hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta isa birnin Kyiv in da za ta gana a wannan Talata da Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine, batun kara yi wa Rasha matsin lamba ta hanyar karfafa takunkuman da aka lafta mata kan mamayar Ukraine da jadada taimakon kasashen Turai ga kasar ta Ukraine da ke kokarin kare martabarta, na daga cikin batutuwan da za su tattauna a wannan ziyarar da ke zuwa a daidai lokacin da Rashan ke bikinta na Victory Day da ta saba gudanarwa a duk ranar tara ga watan Mayu. Babu dai karin bayani kan fatan Ukraine na zama mamba a cikin Kungiyar EU a yayin da take jiran sahalewar kungiyar a hukumance bayan aminta da bukatar a bara.