Amirka ta dakatar da kamfanin sadarwar Chaina
October 27, 2021Amirka ta haramta amfani da layin sadarwar Telecom mallakin China a duk fadin kasar. A sanarwar da ta fitar a yammancin jiya Talata, ta bai wa Chaina wa'adin kwanaki sittin don ganin ta janye daga cikin kasar. Ma'aikatar mai kula da hanyoyin sadarwar ta Federal Communications Commission ko FCC a Amirka, da ta fitar da sanarwar, ta kare matakin bisa zargin cewa, Chaina na iya amfani da hanyar sadarwar a tatsar bayanai da ka iya zame wani babban hadari ga tsaron Amirka.
Miliyoyin Amirkawa ne suka dogara da layukan sadarwar Telecom da ya shafe akalla shekaru ashirin a Amirkan. Akwai fargabar haramcin ka iya haifar da tsamin dangantaka a tsakanin kasashen da ke kokarin farfado da huldar diflomassiyar da ta tabarbare a lokacin tsohuwar gwamnatin Donald Trump.