Takaddama a kan sabon kasafin kudin Amirka
October 5, 2013Sakataren kula da harkokin wajen Amirka John Kerry, ya yi gargadin cewar, tsawaita lokacin takaddamar siyasar da ta barke a kasar, ka iya raunana matsayin Amirka a idon duniya, yayin da matakin rufe harkokin gwamnatin Amirka ya shiga yininsa na biyar kenan a jere. Kerry, ya ambata a wajen taron hadin kan tattalin arziki na kasashen yankin Asiya da Pacific da ke gudana a Bali na kasar Indonisiya cewar, tsawaita lokacin takaddamar, ko kuma maimaita ta, zai sa mutane su fara aza ayar tambayar ko ma Amirka za ta iya zama abar misali ga sauran kasashen, wanda kuma ya ce yana fatan ba za a kai ga wannan yanayi ba.
A halin da a ke ciki kuma, shugaba Amirka Barak Obama ya soke ziyarar da ya shirya kai wa Asiya da kuma wasu manyan tarukan kasa da kasa guda biyu, saboda dakatar da ayyukan gwamnatin Amirka sakamakon takaddama a tsakanin majalisun dokokin kasar a kan kasafin kudi.
Tun dai ranar Talatar da ta gabata (01. 10. 13) ce, ayyukan hukumomi da ma'aikatun gwamnatin da ayyukansu bai zama tilas ba ya tsaya cik sakamakon gaza cimma daidaito a kan sabon kasafin kudin kasar. 'Yan jam'iyyar Republicans da ke da rinjaye a majalisar wakilai na neman shugaba Obama ya jinginar da shirin samar da sauye sauye a sashen kula da lafiyar da yake neman yi, ko kuma hana samar da kudi domin shirin. Ya zuwa yanzu kuma babu wata alamar cewar, takaddama tsakanin majalisar wakilai da ta dattijai a kan batun, ta kusa kawo karshe.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasir Awal