Takaddama a kan gwamnatin kawance a Nijar
August 17, 2013Talla
Jam'iyyar Moden Lumana Afrika ta shugaban majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar Hama Amadou, wadda ke kawance da jam'iyyar shugaba Muhammadu Isuhu, wato PNDS Tarayya, ta bada sanarwar dakatar da ministocinta daga cikin sabuwar gwamnatin hadin kan kasa da shugaban kasar ya kafa a farko-farkon wannan makon.
Jam'iyyar ta ce ta dau wannan mataki ne saboda rashin amincewarta da kason da aka bata a cikin sabuwar majalisar ministocin kasar sai dai jam'iyyar ta ce za ta cigaba da kasancewaa cikin kawancen jam'iyyun da ke milki a kasar.
Mawallafi : Gazali Abdou Tasawa
Edita : Saleh Umar Saleh