1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama a kan dokar ta-baci a Najeriya

May 27, 2013

Batun kudi ya janyo cece-kuce a tsakanin shugaban Najeriya da kuma gwamnonin jihohin da aka sanyawa dokar ta-baci.

https://p.dw.com/p/18dgd
A Joint Military Task Force (JTF) soldier positions his rifle on sand bags on the road in northeastern Nigerian town of Maiduguri, Borno State , on April 30, 2013. Fierce fighting between Nigerian troops and suspected Islamist insurgents, Boko Haram at Baga town in the restive northeastern Nigeria, on April 30, 2013 left dozens of people dead and scores of civilians injured. But the military denied the casualty figures claiming it was exaggerated to smear its image. Meanwhile normalcy has return to the town as residents are going about their normal business. AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Sojan Najeriya dake yaki da Boko HaramHoto: Getty Images/AFP

Tuni dai soja da jami'an tsaro suka cika tudu da kwarin jihohin Borno da Yobe dama Adamawa da gwamnatin tarayyar Najeriyar ta kai ga kakaba wa dokar ta-baci cikin makon jiya. To sai dai kuma daga dukkan alamu tana shirin barin baya da kura ga batun kisan kudin biyan sojojin da cikin kankanen lokaci suka yi nasarar tarwatsa 'ya'yan kungiyar boko haram zuwa gidan buya.

Ra'ayi dai a tsakanin majalisun tarayyar Najeriya biyu na rabe sak ga batun yanda dokar zata gudana da ma yanda za'a kai ga samar da kudin tafi da ita dama tabbatar da mulki a cikin jihohin uku. Cikin kiftawar ido babu bata lokaci dai 'yan majalisar dattawan kasar suka ce sun amince da bukatar shugaban kasar na amfani da kudin jihohin uku wajen aiwatar da dokar da ta bada fifiko ga batun tsaro da zaman lafiya maimakon aiyyuka na raya kasa, abun kuma da ya harzuka yan uwansu na wakilai da suka ce ba zata sabu ba wai bindiga a cikin ruwa. Hon. Ahmed Babba kaita dai na zaman dan majalisar wakilai daga Katsina. Kuma a cewarsa matsalar ta kasa ce ba matsala da shafi jihohin uku ba.

This picture taken on April 30, 2013 shows a Nigerian soldier, part of the 'Operation Flush' patrolling in the remote northeast town of Baga, Borno State. Nigeria's military said on May 16, 2013 that it was ready to launch air strikes against Boko Haram Islamists as several thousand troops moved to the remote northeast to retake territory seized by the insurgents. AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)
Sojan Najeriya dake yaki da Boko HaramHoto: Getty Images/AFP

Siyasa da batun ta baci ko kuma kokari na bada kanwar baki ga tumakin baki dai, ko bayan kokarin gwamantin kasar na kaucewa biyan alawus alawus da ragowar kudaden aikin da dubban sojojin ke matukar bukata dai, wani batu da har ila yau ke neman raba kan yan majalisun na zaman na makomar gwamnoni da shugabannin kananan hukumomin da dokar ta nemi su koma karkashin ikon shugaba Jonathan a kai tsaye amma kuma yan majalisar suka ce da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa.  Abun da ra'ayin majalisun biyu yazo daya kan cewar matakin bai dace da demokaradiyar da tarayyar Najeriya ke gine kai ba.

Description en:House of Representatives of Nigeria Date 16 September 2005, 11:13 Source The House of Representatives Author Shiraz Chakera ou are free: to share – to copy, distribute and transmit the work to remix – to adapt the work Under the following conditions: attribution – You must attribute the work in the manner specified by the author or licensor (but not in any way that suggests that they endorse you or your use of the work). share alike – If you alter, transform, or build upon this work, you may distribute the resulting work only under the same or similar license to this one.
Ginin majalisar dokokin NajeriyaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Ra'ayin majalisar dokoki akan biyan kudin dokar ta-baci

Senator Kabiru Gaya dai na zaman dan majalisar dattawa daga Kano,  Kuma a cewar sa soja bashi da iko na gaban kansa cikin wurin da dokar ke aiki yanzu haka.

To sai dai kuma koma wane irin salo dokar da gwamantin kasar ke yiwa kallon matakin karshe ke iya dauka da nufin kaiwa ga ganin bayan rikicin da ya hallaka mutane kusan 4000 dai, daga dukkan alamu ba ta kai ga burge yan adawar tarayyar Najeriyar dake mata kallon wani kokari na musgunawa wadanda ruwa ya kaiwa iya wuya ba. Abun kuma da a cewar Senata lawalli Shuaibu dake zaman sakataren jam'iyyar A.C.N mai adawa ba zai taimaka wajen kawo karshen matsalar ba.

Har ya zuwa ranar yau dai rahottani na kara karanci game da makomar al'ummar da dokar ke shirin sauya wa zama da kuma ke tsakanin dar dar din tashin hankali na kungiyar Boko Haramun da kuma wuce gona da irin sojan kasar ta Najeriya.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Saleh Umar Saleh