Bala'i
Jamhuriyar Nijar ta amince da dokar kariya kan bala'i
December 6, 2018Talla
Jamhuriyar Nijar ta zama kasa ta farko a nahiyar Afirka da ta amince da shiri na kasa kan kariya da taimakon mutanen da suka tsere daga wuraren da ake samun tashe-tashen hankula da ambaliyar ruwa da fari.
Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin kasar suka tabbatar da haka a wannan Alhamis. Lawan Magagi ministan lamuran jinkai na kasar ya ce kimanin mutane 174,000 suka tsere zuwa kasar ta Jamhuriyar Nijar galibi daga Najeriya da Mali sakamakon rikicin kungiyoyin masu matsanancin kishin addinin Islama. Akwai wasu kasashen da suka amince da wannan kudirin dokar na shekara ta 2009 na Tarayyar Afirka, amma ba su saka cikin dokokinsu ba tukunna.