1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

An taimaki masu kananan sana'o'i

April 11, 2023

A Zinder da ke Jamhuriyar Jamhuriyar Nijar kungiyar da ta kumshi ma'aikatan kafofin sadarwa ta kaddamar da taimako ga masu kananan sana'o'i mata da matasa.

https://p.dw.com/p/4PubX
Jamhuriyar Nijar | Mata
Mata a Jamhuriyar Nijar

A yankin Damagaram na Jamhuriyar Niger wata kungiya ce da ta kumshi ma'aikatan kafofin sadarwa mai sunan OMV wace ke samun tallafi daga wani kamfani mai sunan AIR CABI  SARL ce ke ci gaba da tallafa ma mata da  matasa masu kananan sana'o'in da suka hada da tuyar kosai, awara, masa da dai sauransu domin yin dogaro da kai.

Ita dai kungiyar ta OMV da ma'aikatan kafofin sadarwa ke jagoranta da ake kira (Observatoire des médias pour la vulnérabilité) na sa ido ga masu rauni ta hanyar ba su tallafin kudi a zaman jari domin bunkasa  kasuwancinsu, a bana ka dai kimanin mutane 300 suka ci gajiyar  tallafin, daga ciki  mata na da kaso 75% maza na da kaso 25%. To ko ya suke zabin masu sana'o'in Ousseini Maman shi ne shugaban kungiyar, an tambaye shi kuma wata suke gano mutane, inda ya ce misali mai kosai sai ta ce zuwa take ta kai kudin yau gurin mai sayar da wake kuma ta dauko bashin na gobe, ke nan su ba su da jari, karbowa ce suke su sarrafa su samu dan ribarsu, akwai masu kossai, masu awara, masu fura, masu dan wake da inda kowane shiyya aka dauki mutum hamsin-hamsin.

'Yan mata Fatima mai awara tana daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin na OMV a fuskar mata wadda ta nuna jin dadi da taimakon. Ko baya ga yan mata da kuma mata iyayen marayu da kasuwncin suke tafiyar hawainiya, su kansu su Malam Lawali da kasuwancin da kadan ta dara babu mun samu taimakon.