Tagwayen fashe-fashe a Lebanon | Labarai | DW | 23.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Tagwayen fashe-fashe a Lebanon

Kimanin mutane 19 sun hallaka sakamakon fashe-fashen da aka samu a Lebanon

An samu wasu tagwayen fashe-fashe da suka ratsa birnin Tripoli na arewacin kasar Lebanon. Inda jami'an gwamnatin suka tabbatar da mutuwa tare da jikata wasu mutane.

Rahotanni sun nuna cewa akalla mutane 19, sun hallaka yayin da wasu masu yawa suka samu raunika. Lamarin ya faru yayin da ake ci gaba da samun zaman tankiya cikin kasar ta Lebanon, bisa yakin da ke farauwa a kasar Siriya mai makwabtaka.

Akwai 'yan Shi'a na kungiyar Hezbollah daga Lebanon, wadanda ke tallafawa gwamnatin Shugaba bashar al-Assad.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman