Tafiya Turai bisa hanyar doka | Zamantakewa | DW | 12.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Tafiya Turai bisa hanyar doka

Sakamakon yadda wasu matasa kan nemi shiga kasashen Turai ta barauniyar hanya, wani matashi a Najeriya ya yi suna a wajen horas da matasa wasan kwallon kafa sannan ya dauki dawainiyarsu har zuwa kasashen Turai. 

Wannan matashi Mohammed Babawo, ya dauki tsawon lokaci yana wannan harka, inda matasa da dama suka sami zuwa manyan-manyan kulob-kulob na kasashen duniya, don yin wasan kwallon kafa. 

Ya sheda wa tashar DW cewar yakan duba matasa masu hazaka da fasahar wasan kwallon kafa, kafin daga bisani ya horas da su tun daga gida Najeriya har zuwa ketare.

Kasancewar Mohammed Babawo dan arewacin Najeriya ne, kuma yakan dauki dawainiyar matasa 'yan arewa da ma na kudancin Najeriya, ya ce kawo yanzu ya horas da matasa 'yan kudancin Najeriya irin su Uche Obodo, Obinna Nwsofo, da su John Mikel Obi. 

Cikin irin yara matasa da Babawo ya horas, akwai Suleiman Mohammed wanda aka fi sani da Yaro, da jima yana sha'awar ya je Turai kafin daga bisani ya sami zarafi ta hanyar Mohammed Babawo.

Daya daga cikin ire-iren matasan da ke jiran shiga Turai ta hanyar Babawo, akwai Abduljabbar Sani, wanda aka fi sani da Baba Gaye, ya yi wa DW karin haske kan cewa tun lokacin da ya samu saduwa da Babawo yake da kwarin gwiwa burinsa na zuwa Turai zai cika, ganin irin a tarihance mutanen da suka bi ta hannun Babawo, kana suka samu tsallakawa zuwa Turai a ka'idance.

Mohammed Babawo dai ya ce babban burinsa shi ne janyo hankulan matasa 'ya'yan talakawa, domin ya tsallakar da su zuwa Turai, a hanyar wasan kwallon kafa, domin samun abin dogaro a rayuwa. Inda su ma a bisani za su taimaka wa 'yan baya masu tasowa.