Tabarbarewar tsaro a Najeriya duk da bunkasar tattalin arziki | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 18.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Tabarbarewar tsaro a Najeriya duk da bunkasar tattalin arziki

Masu mulki da na kusa da su ke cin amfanin bunkasar tattalin arzikin kasar, yayin da ake kawar da duk mai kokarin bankado almundahana da ke faruwa.

A wannan makon dai jaridun sun fi mayar da hankali ne a kan tabarbarewar tsaro a tarayyar Najeriya.

A labarinta mai taken bunkasar tattalin arziki maras riba, jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi.

"Bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar cewa bisa alkalumman da tattara yanzu sun nuna cewa kasar ce mafi karfin tattalin arziki a nahiyar, sai ga shi an samu tashin bam a birnin Abuja, wanda ya hallaka mutane da yawan gaske. Sannan a lokaci daya 'yan bindiga sun yi garkuwa da 'yan matan wata makaranta a arewacin kasar. Wannan ba abin mamaki ba ne a wata kasa irin Najeriya, to amma bambamci tsakanin labari mai fararta rai da mai bakanta rai a kwanakin nan ya nuna cewa akwai mummunan abu a cikin tsarin tafiyar da kasar. Masu mulki da 'yan korarsu ke cin amfanin bunkasar tattalin arzikin kasar, kuma duk wanda ya fito fili ya yi suka sai an ga bayanshi kamar yadda a cikin wata Fabrairu shugaba Goodluck Jonathan ya dakatar da gwamnan babban bankin kasar bayan kalaman da ya yi cewa dubban miliyoyin kudaden mai sun bace."

Karancin ilimi na daga cikin dalilan rashin tsaro

Wata kungiya ta addabi Najeriya inji jaridar Der Tagesspiegel tana mai cewa kungiyar Boko Haram na kara yin karfi a Najeriya, amma masana na ganin karancin ilimi da yawan al'umma da ba su da abin yi su ne musabbabin karuwar tashe-tashen hankulan a tarayyar ta Najeriya.

Die Bettel-Schüler aus Nordnigeria

Gwamnatin Najeriya ta kuduri aniyar mayar da makarantun allo zuwa na zamani

"A farkon wannan mako birnin Abuja ya ga mummunan tashin hankali na fashewar bam a babbar tashar motocin bas da ke wajen garin. Wannan ya faru ne bayan wasu hare-hare da aka kai kan wasu kauyuka uku na jihar Borno, da ke yankin arewa maso gabacin kasar, inda tun farkon shekara kungiyar Boko Haram ta tsananta ayyukanta. Sannan kwana daya baya aka yi garkuwa da dalibai mata fiye da 100 a wata makarantar sakandare da ke a wannan jiha. A kullum wadannan hare-haren da ake danganta su da kungiyar Boko Haram sai karuwa suke yi, yayin da mahukuntan kasar ke ikirarin samun galaba a kan 'yan tarzoma, abin da har yanzu ba a gani a kasa ba. Najeriya dai kasa ce mai yawan matasa, sai dai masana na masu ra'ayin cewa Najeriya ba za ta kasance daya daga cikin kasashe mafi yawan matasa a duniya ba, a a tana iya kuma zama mafi hadari a duniya."

Kame-kamen babu gaira a Ruwanda

Paul Kagame Präsident Ruanda

Shugaba Paul Kagame na Ruwanda

Mawaki a matsayin dan ta'adda? Tambayar da jaridar Die Tageszeitung ta yi ke nan lokacin da take tsokaci kan matakin da hukumomin kasar Ruwanda suka dauka na kame sanannen matashin mawakin kasar bisa zarginsa da hada baki da sojojin sa kai da suka aikata kisan kiyashi a kasar.

"Tare da wani abin mamaki an kammala zaman alhinin na tsawon mako guda na cika shekaru 20 da kisan kare dangin da ya auku a Ruwanda. An kame Kizito Mihigo daya daga cikin mashahuran mawakan kasar wanda kanshi ya tsira daga ta'asar kisan kare dangin, bisa zarginsa da taimaka wa shirin kai hare-hare ta'addanci. An kamashi ne tare da Cassien Ntamuhanga daraktan gidan rediyon watsa shirye-shiryen addinin Kirista da akwun gidan rediyon da kuma wani soja. Shi dai Kizito Mihigo ya shahara a kasar ta Ruwanda bisa wakokinsa na neman zaman lafiya da yafe wa juna. Saboda haka kama shi bisa zargin ta'addanci ya zo da mamaki."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe