1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: Tsarin masarautar Damagaram

Salissou Boukari AH
October 30, 2018

Masarautar Damagaram a gabashin Jamhuriyar Nijar na yin aiki da tsari na gargajiya da kuma na zamani wadanda dukka biyu suka yi tasiri wajen ci gaban masarutar.

https://p.dw.com/p/37NoR
Palast des Emirs von Damagaram in Zinder, Niger
Masarautar DamagaramHoto: DW/M. Kanta

Mai martaba sarkin Damagaran Sultan Aboubacar Oumarou Sanda a cikin tattaunawar da aka yi shi a cikin shirin Taba Ka Lashe ya tabbatar da cewar masarautar wace ta samo tushe tun kafin zuwan 'yan mulkin mallaka, na da al'adunta wadanda aka dade ana yin aiki da su.

Aboubacar Oumarou Sanda, Sultan von Damagaram/Niger
Suktan Aboubacar Oumarou Sanda, sarkin DamagaramHoto: DW

Sai dai kuma ya ce da yake zamani ya sauya don haka dole suka sauya tsari don  yin daidai da zamanin domin jin dadin al'umma. Mai martaba Sultan Aboubacar Oumarou Sanda ya ce babban sakon da ke gareshi a wajen al'umma shi na tabbar da samar da zaman lafiya da kuma girmama al'adu na yankin.