Taba ka Lashe: Tattalin wakokin Afirka zalla | Zamantakewa | DW | 18.12.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Taba ka Lashe: Tattalin wakokin Afirka zalla

A Jamhuriyar Nijar mawaka da makada na gargajiya da na zamani na kasashen Afirka sun kaddamar da cibiya ta hadin gwiwa ta raya da bunkasa harkokin wakoki da mawakan Afirka zalla mai suna African Music Confederation.

Burin da aka sa gaba a nan shi ne sake farfado da martabar wakokin nahiyar ta Afirka da ma sauran kasashen duniya. A cikin shirin na Taba ka Lashe da ke duba batutuwan da suka shafi al'adu da addinai da zamantakewa, za mu duba irin tasirin da kungiyar za ta yi wajen karfafawa mawaka gwiwa da bunkasa al'adun gargajiyar nahiyar ta Afirka.

Babban burin da mawaka da makada na gargajiya da na zamani na nahiyar Afirka suka sa gaba dai shi ne bullo da wani sabon tsari da samfuri da zai hada kan mawakan daga sassa daban-daban na Afirka musamman wajen bunkasa al'adun gargajiya na kasashen nahiyar ta Afirka.

Sabeïba-Tänzer mit Schwert Flash-Galerie (picture-alliance/Désirée von Trotha)

Malam Abdul-Salam daya ne daga cikin mawakan da ke wakiltar Nijar ya ba da dan takaitaccen tarihi dangane da wannan tafiya da aka sa gaba. Ko wasu kasashe ne baya ga Nijar da Benin da ke cikin wannan kungiya ta mawaka da makada na Afirka zalla, kuma wani buri a kasa a gaba?

Kasashen Afirka dai na da dinbim mawaka da tarin al'adu wadanda kuma idan suka hada kai suka jajirce za su iya cirewa kansu kitse daga wuta, musamman wajen bunkasa al'adun al'ummomin nahiyar ta Afirka da ma fidda sunan kasashen a fagen kade-kade da wake-wake na duniya. A bisa wannan dalili ne jagororin kungiyar ta hadin gwiwar mawakan Afirka suka bayyana wani mataki na shirya gasar cin kofin zakarun mawaka da makada daga ko ina cikin kasashen Afirka. Mache Viktor Fodji shahararren mawaki ne daga Benin da ya nuna amfanin wannan gasa.

Saurari sauti 09:40

Taba ka Lashe: Tattalin wakokin Afirka zalla

Tuni dai wasu masana harkokin al'adu suka bayyana gamsuwa da wannan mataki na samar da cibiyar hadin gwiwa da za ta raya tare kuma da bunkasa harkokin wakoki da mawakan Afirka zalla wato African Music Confederation. Mal. Rabo Mato mai sharhi ne a kan al'amuran bunkasa al'adu kuma tsohon ma'aikaci a hukumar bunkasa ilimi, kimiyya da al'adu ta MDD wato UNESCO, ya bayyana cewa matakin da mawakan suka dauka na iya yin tasiri. Don jin cikakken shirin ana iya latsa shirin na sauti.

Sauti da bidiyo akan labarin