1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubalen sana'ar wanzanci a Afirka

Suleiman Babayo LMJ
January 22, 2019

Shirin na wannan lokaci ya yi nazari kan daya daga cikin sana'o'in Hausa na asali wato "Wanzanci" da zamani ya mamaye yake neman kawowa wannan sana'a da ta dade tana tasiri a tsakanin al'umma tarnaki.

https://p.dw.com/p/3BzR3
EURO 2016 Spielerfrisuren Paul Pogba
Yanayin askin zamaniHoto: picture-alliance/Back Page Images/

Wanzamai mutane ne da suke gudanar da sana'a da aka sani a kasar Hausa, inda suke kan gaba wajen yi wa yara kaciya musamman maza da aski da wasu abubuwan da suka danganci lafiya, amma mutane galibi sun koma asibitoci sannan aski da ya rage a hannun wanzaman, sannan za a iya cewa masu aski na zamani sun yi kakak gida a bangaren askin. Shugaban wanzamai da ke binrin Yamai na Jamhurriyar Nijar, Moussa Wansaba ya ce har yanzu ana samun yaran da suke yi wa kaciya, kuma a irin wannan lokaci na hunturi galibi ake yin kaciyar, sai dai ya ce daya daga cikin matsalolin da ake gani idan sun yi kaciya ga yara maza shi ne katsalandan da wasu ke yi wa sana'ar. Ku biyo mu a cikin shirin.