Taba Ka Lashe: 10.+11.02.2016 | Al′adu | DW | 11.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Al'adu

Taba Ka Lashe: 10.+11.02.2016

Kamar a kowace shekara a bana ma an gudanar da bikin al'adu na Karnival a wasu sassa na Jamus, amma an soke gudanar da faretin ranar Litinin saboda rashin kyaun yanayi.

Sai dai a bana an soke gudanar da bikin a wasu manyan garuruwa irinsu Düsseldorf da Mainz da ke zama cibiyoyin bikin saboda rashin kyaun yanayi. Sannan a birnin Kolon da aka gudanar da bikin, bikin bai yi armashi sosai ba domin an hana hawa dawakai da amfani da manyan mutum mutumin da ke kara wa bikin launi. An kuma tsaurara matakan tsaro musamman biyo bayan cin zarafin wasu mata da aka yi a birnin Kolon a daren shiga sabuwar shekara.

Sauti da bidiyo akan labarin