1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 01.08.2018

Mohammad Nasiru Awal
August 3, 2018

'Yan ci-rani daga Afirka da ba su da takardun izini zama a kasa na amfani da lokacin hutun bazarar domin sayar da kayayyakin tsaraba ga 'yan yawon shakatawa a gabar tekun Spaniya.

https://p.dw.com/p/32al4

A daidai lokacin ake fama da tsananin zafi a fadin nahiyar Turai, kuma masu yawon bude ido ke turuwa zuwa kudanci nahiyar don hutu na lokacin bazarara, hada-hada ta kankama a yankin gabar teku na kudancin kasar Spaniya. 'Yan ci-rani daga nahiyar Afirka wadanda ba su da takardun izini zama a kasa na amfani da wannan dama domin sayar kayayyaki da yawansu na jebu ne, ga 'yan yawon bude idon. A wannan makon shirin ya yi tattaki zuwa yankin Fuengirola da ke bakin tekun kasar Spaniya.