1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake rufe makarantun 'yan mata a Afghanistan

March 23, 2022

Gwamnatin Taliban a Afghanistan ta ba da umurnin rufe makarantu sakandre da na kwaleji na 'yan mata, sa'o'i kadan bayan bude makarantun a hukumance.

https://p.dw.com/p/48vzL
Taliban ordnen die Schließung von Mädchenoberschulen in Afghanistan an
Hoto: Ahmad Sahel Arman/AFP/Getty Images

A  larduna da dama,an bude makarantu kuma aka sake rufesu in ban da na Kandahar da ke a kudancin kasar inda  nan ne cibiyar 'yan Taliban din, wanda sai cikin wata mai zuwa aka shirya za a bude makarantu a can. 'Yan makaranta wadanda suka koma bokon a karon farko tun bayan  da masu kishin adinin suka karbe mulki a cikin watan Agustan da ya gabata. Sun rufe littattafansu, suka kwashe kayayyakinsu, suka bar ajin suna kuka. Yayin da wasu suka ƙi ficcewa daga harabar makarantu kamar yadda kamfanin dilancin labarai na faransa AFP ya shaida.'Yancin mata na neman ilimi dai, na daya daga cikin manyan sharuddan kasashen duniya, na ba da taimako ga gwamnatin da ba a amince da ita ba, ta Kabul .