Taɓa Ka Lashe: 13.01.2010
January 19, 2010Talla
A kowace shekara bayan sallar laiya, al´umar jihar Agadez a janhuriyar Nijer na gudanar da bikin al´adun gargajiya na Biano. Wannan bikin dake zama ɗaya daga cikin bukukuwan al´adun gargajiya a Agadez, ya na da dadaɗɗen tarihi kuma ana danganta shi da bikin Ashura.