Taƙaddamar iko da garin Goma | Labarai | DW | 29.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taƙaddamar iko da garin Goma

Dakarun Kongo sun bayyana kimtsawa domin ƙwace iko da garin Goma da ke hannun 'yan tawaye.

A ranar wannan Alhamis ce sojojin jamhuriyyar Dimoƙraɗiyyar Kongo suka isa kusa da garin Goma da ke yankin gabashin ƙasar, wanda kuma ke hannun 'yan tawayen ƙasar, inda jagorar dakarun gwamnatin ya ce a shirye mayaƙansa suke su gwabza yaƙi domin neman ƙwato Goma daga hannun 'yan tawayen, waɗanda suka yi watsi da wa'adin ficewa daga birnin da aka ba su a can baya.

Hafsan sojin gwamnatin janar Francois Olenga ya faɗi a garin Minova, da ke da tazarar kilomita 50 daga birnin na Goma cewar a yanzu dai tura ta kai bango, kuma tuni ya baiwa dakarunsa umarnin su shirya shiga yaƙi. Ya ƙara da cewar bai kamata a ci gaba da yin kwan gaba kwan baya ba wajen ƙokarin neman sulhu, abinda ya rage kawai shi ne gwabza yaƙi, wanda ka iya kaiwa ga zaman lafiya a ƙasar.

Dama dai shugabannin ƙasashen yankin Great Lakes, da kuma tawagar ƙungiyar tarayyar Afirka da suka gana a ƙasar Uganda a ƙarshen mako ne suka umarci 'yan tawayen su fice daga birnin a ranar Litinin, amma kuma suka yi watsi da wannan umarnin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Halima Balaraba Abbas