Syriya na neman a dakatar da buɗe wuta | Labarai | DW | 20.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Syriya na neman a dakatar da buɗe wuta

Mataimakin firaminista na Syriya Qadri Jamil ya bayyana cikin wata hira da jaridar The Guardian cewa a shirye gwamnatinsa ta ke ta tsagaita bude wa 'yan tawaye wuta.

Syriya ta yi gargaɗin cewar a shirye ta ke ta nemi a kawo ƙarshen yaƙin da ta ke yi da' yan tawaye a gaban taron ƙasa da ƙasa da za a yi a birnin Jeniva . Wani babban jami'in gwamnatin Qadri Jamil shi ne ya bayyana haka a lokacin wata tattaunawa da jaridar The Guardian.

Jamil ya ce a akwai buƙatar a dakatar da yaƙin saboda daga dukkanin ɓangarorin biyu babu wani wanda ke da ƙarfin samun nasara a faɗan. Mutane dai kusan dubu ɗari ne suka rasa rayukansu a yaƙin na Syriya,kuma ministan ya ce ya zuwa yanzu sun kashe kuɗaɗe sama da miliyan dubu ɗari saboda yaƙin.

Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe