Syriya na neman a dakatar da buɗe wuta
September 20, 2013Talla
Syriya ta yi gargaɗin cewar a shirye ta ke ta nemi a kawo ƙarshen yaƙin da ta ke yi da' yan tawaye a gaban taron ƙasa da ƙasa da za a yi a birnin Jeniva . Wani babban jami'in gwamnatin Qadri Jamil shi ne ya bayyana haka a lokacin wata tattaunawa da jaridar The Guardian.
Jamil ya ce a akwai buƙatar a dakatar da yaƙin saboda daga dukkanin ɓangarorin biyu babu wani wanda ke da ƙarfin samun nasara a faɗan. Mutane dai kusan dubu ɗari ne suka rasa rayukansu a yaƙin na Syriya,kuma ministan ya ce ya zuwa yanzu sun kashe kuɗaɗe sama da miliyan dubu ɗari saboda yaƙin.
Mawallafi :Abdourahamane Hassane
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe