Sulhunta siyasar Kinsha ya wargaje
September 23, 2016Talla
Tattaunawa sasanta rikicin kasar Kongo ya wargaje ne, bayan da bangaren adawan a yau Juma'a suka fidda sanarwar janyewa daga tattauanawar, inda suka ce farmakin da jami'an tsaro suka kai, wanda ya hallaka sama da mutane 50, ya nuna alamun gwamnati bata da shirin sulhu, kuma dole ake so sai shugaba Joseph Kabila ya zarce, Duk kuwa da karewar wa'adin mulkinsa. Su dai 'yan adawa na neman shugaba Kabila wanda ke mulkin kasar tun shekara ta 2001, da ya sauka daga mulkin, inda wa'adin mulkin sa ke karewa a ranar 20 ga watan Disamba, amma kuma babu ranar gudanar da sabon zabe.