Sulhun sojoji da gwamnati a cote d′Ivoir | Labarai | DW | 12.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sulhun sojoji da gwamnati a cote d'Ivoir

Bayan boren da wasu sojoji suka yi a watannin baya, domin neman a biya su wasu kudade na alawus-alawus dinsu, sojoji 8.400 a kasar Cote-d'Ivoir sun nemi gafara ga 'yan kasa.

Elfenbeinküste Meuternde Soldaten halten Verteidigungsminister fest (Getty Images/AFP/S. Kambou)

Sojojin Cote d'Ivoir lokacin da suka yi bore

Sojojin sun bayyana janye bukatar tasu ne, yayin wata gana wa da suka yi da shugaban kasar Alassane Ouattara a fadarsa da ke birnin Abijan. Shugaba Ouattara ya ce ya yi imani da gaskiyar wannan magana ta sojojin, inda kuma ya ce babu shakka za su kasance sojoji na gari. An dai wallafa wannan haduwa ta gidan talbijin din kasar ta Cote d'Ivoir, kuma sojojin sun ce sun dauki alkawarin yin ladabi da biyayya ga kasa kamar yadda aka sani a tsarin ayyukansu na sojoji. Sojojin dai da ke bukatar alawus na miliyan 12 na CFA, sun samu miliyan biyar a watan Janairu da ya gabata, inda ya kamata su karbi sauran da ya rage a watan Janairu mai zuwa amma suka ce sun bar wannan batu. Sai dai har yanzu akwai rade-radin cewa akwai wasu yankunan kasar da rikicin sojojin ke ci gaba.