Sulhu a tsakanin Isra′ila da Falasdinu | Labarai | DW | 21.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sulhu a tsakanin Isra'ila da Falasdinu

Isra'ila ta ce za ta yanke wasu shawarwari masu ban mamaki a tattaunawarta da Falasdinu.

Bayan gudanar da wani zagaye na tattaunawa a tsakanin Falasdinu da Isra'ila a wannan Talatar (20.08.13), kuma duk da cewar daukacin sassan biyu sun yi alkawarin kin bayyanawa jama'a irin abubuwan da suka cimma, jagorar wakilan Isra'ila a wajen tattaunawar, kana ministar shari'ar kasar Tzipi Livni, ta sanar ta wata tashar rediyon Isra'ila cewar, kasar za ta yanke wasu muhimman shawarwari na ban mamaki domin cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta karshe da Falasdinu. Ta kuma nuna takaicinta dangane da rashin samun goyon baya ga tataunawar, daga bangaren masu tsattsauran ra'ayin da ke cikin gwamnatin kawancen kasar, a karkashin fira minista Benjamin Netanyahu. Wannan tattaunawar dai, sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ne ya tsara, a karon farko cikin tsukin shekaru biyar. Dama tun a shekara ta 2008 ne, tattaunawar ta katse, sakamakon takaddama a kan batutuwan da suka hada da samar da karin matsugunai a yankunan da Falasdinawa ke fatan ya kasance kasarsu a nan gaba, wanda hukumomin na Isra'ila ke yi.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu