Sudan ta Kudu ta saki wasu fursunonin siyasa | Labarai | DW | 29.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta Kudu ta saki wasu fursunonin siyasa

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta miƙa fursunoni guda bakwai magoya bayan Riek Machar ga hukumomin ƙasar Kenya.

Sai dai duk da haka gwamnatin ta dage cewar za ta gurfanar da wasu mutane guda fuɗu da ta ke ci gaba da tsare su a gaban kotu a kan yunƙuri yi wa shugaba Salva Kiir juyin mulki.

A cikin mutane da aka sako har da tsohon ministan shari'a wanda aka kora daga gwamnatin a cikin watan Yulin da ya gabata tare da Riek Machar. Yayin da sauran waɗanda suka haɗa da tsohon ministan tsaro da tsohon sakataran jam'iyyar da ke yin mulki da kuma tsohon jakadin ƙasar a Amirka za a yi musu shari'a. A makon jiya ne masu shiga tsakani a rikicin suka ce an cimma yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu, kuma ɗaya daga cikin batutuwa da aka amince da su a yarjejeniyar, shi ne na sakin 'yan tawayen da ake tsare da su.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal