Sudan Ta Kudu ta dauki hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 03.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Sudan Ta Kudu ta dauki hankalin jaridun Jamus

Batun shawarwari kan rikicin Sudan Ta Kudu da kisan gilla ga dan adawar Ruwanda suna daga cikin al'amuran da jaridun Jamus suka maida hankali kansu a wannan mako

To madallah. Daga cikin al'amuran da jaridun na Jamus suka maida hankali kansu a wannan mako, har da halin da ake ciki a kasar Sudan Ta Kudu, inda ake kokarin hana fadan da ya barke tsakanin gwamnatin shugaban kasa Salva Kiir da tsohon mataimakinsa, Riek Machar ya rikide zuwa ga yakin basasa. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace bayan shiga tsakani da Kungiyar Kadin Kan Gabashin Afirka, wato IGAD tayi, bangarorin biyu na rikicin Sudan Ta Kudu sun fara tattaunawar neman sulhu tsakaninsu a birnin Addis Ababa. Tun kafin a shiga shawarwarin, sai da wakilan bangarorin biyu suka gana a wawware tare da tawagar IGAD, yadda za'a sami makama a wadannan shawarwari. To sai dai kamar yadda jaridar ta nunar, duk da wannan ganawa, yan tawayen suna ci gaba da kokarinsu na neman kwace yankunan kasar ta Sudan Ta Kudu. Bayan da suka mamaye garin Bor dake kudancin kasar sun kama hanyar neman isa Juba, dake da nisan kilomita 200 a kudancin Bor. Tun bayan samun mulkin kanta daga hannun Sudan a shekara ta 2011, kasar ta Sudan Ta Kudu take fama da fadi-tashi, ko dai tsakanin ta da makwabciyarta a arewa ko kuma sakamakon rashin fahimta tsakanin yan siyasa na cikin gida, abin da a yanzu ma ya kai ga yaki tsakaninsu.

Jaridar Die Welt ta tabo kisan gilla da aka yiwa tohon shugaban hukumar leken asirin kasar Ruwanda Patrick Karegeya a wani dakin Hotel a Afrika ta kudu, inda yake zaman hijira tsawon shekaru shida. Jaridar tace yan adawar Ruwanda sun yi karar cewar shugaban kasa Paul Kagame shine ya bada izinin kashe tsohon shugaban hukumar leken asirin. Kagame tun shekara ta 2000 yake rike da mukamin shugaban kasa a Ruwanda. Ko da shike a hannu guda, ya taimakawa kasar a samun bunkasar tattalin arziki, amma a daya hannun, kungiyoyi kare hakkin yan Adam masu tarin yawa suna zarginsa da matakan keta hakkin jama'a, musamman rashin imani kan yan adawa. Karegeya ya dade a matsayin na hannun daman Kagame, kafin a rage masa mukami zuwa kakakin sojan kasar, sa'annan daga baya aka jefa shi gidan kaso, kafin ya tsere zua gudun hijira a shkara ta 2007.

Somalia tödlicher Autobombenanschlag auf Hotel in Mogadischu

Harin bom mai tsanani a Somaliya

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta tabo hare-haren bama-bamai ne a Mogadishu, babban birnin Somaliya da kuma irinsu da aka kai kasar Kenya ranar Talatar da ta wuce. Karkshin taken: bama-bamai da gurnati a ranar sabuwar shekara, jaridar tace kungiyar yan tawayen Somalia, Al Shabaab ita ce ake zargi da wannan danyen aiki, ko da shike ita kanta kungiyar tace harin Somaliya kadai take da alhakin kaishi. Wadannan hare-hare ba zasu rasa dangantaka da gwagwarmayar da kungiyar Al Shabaab take yi ba, na ganin Kenya da sauran kasashe makwabta sun kwashe sojojin da suka tura zuwa Somaliya, kasar da bata da wata tsayayyar gwamnati tun bayan kayar da shugaba Siad Barre a shekara ta 1979.

A nata sharhin, jaridar Neues Deutschland ta duba iin rawar da Faransa take takawa ne a rikice-rikicen yankin tsakiyar Afrika. Jaridar ta duba jawabin sabuwar shekara da shugaban Faransa, Francois Hollande ya gabatar, inda ya tabo shisshigin sojojin kasarsa a Mali da Jamhuriyar Afirka Tsakiya. Yace alhakin Faransa ne ta taimakawa wadannan kasashe a duk lokcin da suke bukatar taimako. To sai dai abin da Hollande bai fada ba, wanda kuma manema labarai suka dade suna neman ji daga bakinsa shin, kasancewar sojojin na Faransa a Afirka bai isa hana kara munin halin rayuwa a wadannan kasashe ba.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Usman Shehu Usman