Su wane ne jiga-jigan gwamnatin Joe Biden?
Shugaban Amirka, Joe Biden, ya fara sanar da sunayen mutanen da zai bai wa mukamai a sabuwar gwamnatinsa. Da yawa daga cikinsu dai sun yi aiki a gwamnatin tsohon shugaban kasar Barack Obama.
Antony Blinken: Sakataren harkokin waje
Antony Blinken tsohon aminin Joe Biden ne. Ya yi aiki a gwamnatocin jam'iyyar Democrats har sau biyu, tare da zama jigo a kwamitin kula da harkokin kasashen waje a majalisar dattawa. Blinken ya kuma taba zama mataimakin mai taimaka wa tsohon shugaban Amirkan Obama a harkokin tsaro da mataimakin sakataren harkokin wajen Amirka, duk a tsohuwar gwamatin da Biden ke zaman mataimakin shugaban kasa.
Janar Lloyd Austin: Sakataren tsaro
Nada Janar Lloyd Austin zabi ne mai sarkakiya. Kasancewar sa dadadden jami'in soja, ya sa tilas sai majalisa ta daga masa kafa kafin a kai ga tabbatar da shi. Austin dai ya sha rike muhimman mukamai lokacin da yake sojan Amirka. Ya yi aiki da gwamnatin Obama lokacin da aka janye sojojin Amirkan daga Iraki. In ya dace, zai zama bakar fata na farko da zai jagoranci ma'aikatar tsaro ta Pentagon.
Janet Yellen: Sakatariyar Baitul Mali
Mace ta farko da za a tabbatar kan wannan muhimmin mukami, ya sanya ganin kyan yunkurin Shugaba Biden na kafa gwamnatin masana da masu asali dabam-dabam. Yellen ta yi aiki a kwamitin tsare-tsare a babban bankin Amirka a shekara ta 2008. Ta bai wa tsohon shugaban kasar Bill Clinton shawarwari lokacin da aka shiga matsin tattalin arziki kamar yadda Amirkan ke cikin yanayi mafi muni a fannin a yanzu.
Ron Klain: Shugaban ma'aikata a fadar White House
Tsohon hannu a Washington DC, Ron Klain ne mutumin da Shugaba Biden ya fara zaba. Zai yi aiki kud-da-kud da shugaban kasa. Shi ne kanwa uwar gamin sabuwar gwamnatin. Shi dai Klain ya taba aiki da Shugaba Biden lokacin da yake mataimakin shugaban kasa a gwamnatin Barack Obama. Klain ya jagoranci aikin yaki da cutar Ebola da aka yi wa lakabi da ''Ebola Czar.''
Xavier Becerra: Sakataren Lafiya
Babban lauyan gwamnatin jihar California, shi ne wanda Shugaba Biden yake son ya jagoranci lafiya, a daidai lokacin da duniya ke fama da babban kalubale a fannin lafiya. Xavier Becerra ya taka rawar gani yayin samar da dokar kiwon lafiya mai rangwame lokacin yana dan majalisa. Idan har majalisar dattawa ta amince da shi, zai kasance mutum na farko daga Latin Amirka da zai rike wannan mukamin.
John Kerry: Manzo na musamman kan sauyin yanayi
Tsohon sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry, zai tsaya wa kasar a harkokin sauyin yanayi. Tsohon sanata ne na Massachusetts daga shekarar 1983 zuwa 2013, kafin ya zama babban jami'in diflomasiyyar kasar a zamanin gwamnatin Obama. John Kerry ne ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar kare muhalli ta birnin Paris a 2015, yarjejeniyar da tsohon shugaban kasar Trump ya fice bayan shekaru biyu.
Linda Thomas-Greenfield: Jakadiyar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya
Linda Thomas-Greenfield ta taba rike babban mukami a ma'aikatar harkokin wajen Amirka a zamanin gwamnatin Shugaba Obama a tsakanin shekarun 2013 zuwa 2017. Ta jagoranci ayyukan da Amirka ta yi a Afirka, a lokacin da cutar Ebola ta barke. Shugaba Biden na shirin dawo da wannan mukamin zuwa fadar gwamnatin Amirkan ta White House.
Alejandro Mayorkas: Sakataren tsaron cikin gida
Ba'amirke mai asali daga Cuba, ya taba rike ma'aikatar shige-da-ficen Amirka a lokacin da Obama ke mulki. Alejandro Mayorkas, ya jagoranci shirin kare matasa da yara baki a kokarin da aka yi na korar su daga kasar a shekarun baya. In har majalisa ta amince da nadin nasa, zai kasance mako kuma dan Latin Amirka na farko da zai rike wannan matsayi na tsaron cikin gida a Amirka.
Jake Sullivan: Mai ba da shawara a kan tsaro
Sullivan ya kasance mai bai wa Biden shawara a kan harkokin tsaro daga shekara ta 2013 zuwa 2014 lokacin da Biden ke matsayin mataimakin shugaban kasa. Ya kuma kasance mataimakin Hillary Clinto lokacin da take rike da mukamin sakatariyar harkokin waje, kafin daga bisani ya zamo mai ba ta shawara kan harkokin kasashen waje, yayin da ta tsaya takarar shugabancin kasar da ba ta yi nasara ba a 2016.
Avril Haines: Daraktar Hukumar Leken Asiri ta CIA
Avril Haines ita ce mace ta farko da ta taba zama mataimakiyar darakta a Hukumar Leken Asirin Amirka wato CIA, mukamin da ta rike daga shekarar 2013 zuwa 2015. Ta gaji Antony Blinken a matsayin mataimakiyar darakta a hukumar a lokacin da Blinken din ya koma mai ba da shawara a kan harkokin tsaro a 2015. Idan ta dace, za ta zama mace ta farko da za ta jagoranci ayyukan leken asiri a Amirkan.