Stephen Keshi ya rasu | Labarai | DW | 08.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Stephen Keshi ya rasu

Stephen Okechuku Keshi tsohon mai horas da 'yan wasan Najeriya kana tsohon kyaftin na ƙungiyar wasannin ƙwallon kafa na Najeriya watau Super Eagles ya mutu da ciwon bugon zuciya.

An ba da rahoton cewar tsohon mai horas da 'yan wasan Najeriya kana tsohon kyaftin na ƙungiyar wasannin ƙwallon ƙafa na Najeriya watau Super Eagles.Stephen Okechuku Keshi ya rasu a tsakiyar daren jiya Talata a birnin Benin na jihar Edo.

Hukumar ƙwallon kafa ta Najeriya ta tabbatar da mutuwar tsohon kyaftin ɗin na Najeriya a shafinta na Twiter inda ta miƙa ta'aziyyarta ga ɗaukacin ‘yan Najeriya.