Sri Lanka: ′Yan kunar bakin wake 7 ne suka kai hare-hare | Labarai | DW | 22.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sri Lanka: 'Yan kunar bakin wake 7 ne suka kai hare-hare

Wasu 'yan kunar bakin wake 7 ne suka kaddamar da hare-haren da suka lakume rayuka 290 a yayin da gwamnatin kasar ta janye dokar hana fita da ta sanya a birnin Colombo da ke cikin jimami a sanadiyyar ayyukan ta'addanci.

Rayuka 290 suka salwanta yayin da wasu fiye da 500 suka sami rauni a jerin hare-haren da aka kai kan coci-coci da otel-otel da suka jefa kasar cikin yanayi na jimami tare da fargabar barkewar rikici na kabilanci. Tuni ma dai rahotanni ke nuni da cewa an kai wasu hare-hare da ake ganin na ramuwar gayya ce a wani yanki da ke arewa maso yamma na kasar a daren ranar Lahadi.

A wannan Litinin shugaban kasar Mai-thri-pala Siri-sena ya kira wani taro na gaggawa da ya hada da kwamitin tsaro.

Kawo yanzu babu kungiyar da ta fito ta dauki alhakin kai wadannan hare-haren a yayin da mabiya addinin kirista kamar sauran kasashen duniya ke tsakiyar bikin Easter, daya daga cikin manyan bukukuwan mabiya wannan addini a duniya.