1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin 'yan gudun hijira ya isa Spaniya

Abdul-raheem Hassan
June 17, 2018

Wani jirgin ruwan kasar Italiya dauke da bakin haure 274 da aka ceto a Tekun Medeterenian, ya isa tashar ruwa na Valancia da ke kasar Spaniya.

https://p.dw.com/p/2ziD1
Spanien «Aquarius»-Migranten in Valencia erwartet
Hoto: Reuters/SOS Mediterranee

Matakin da kasar Spaniya ta dauka na karbar bakin hauren, ya raba gardama da ya kunno kai tsakanin kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Turai kan kasar da zata sauke su. A yanzu 'yan gudun hijiran na samun kulawan gaggawa daga kungiyoyin agaji, yayin da kungiyar Red Cross ta ba da tabbacin isowar sauran jiragen Aquairus na kasar Italiya da ke aikin agaji nan ba da jimawa ba.

Da farko dai kasahsen Malta da Italiya sun ki ba wa jiragen da 'yan gudun hijira 630 ke ciki damar yada zango a kasashen su. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan gudun hijira kusan 1,000 ne suka mutu a ruwa cikin wannan shekara.