Spain da Brazil da kuma Mexico za su taimakawa Cuba
April 19, 2026
Talla
Kasashen Spain da Brazil da kuma Mexico sun yi alkawari kara inganta ayyukan jin kai domin taimakawa kasar Cuba. Kasashen uku sun ce Cuba ta fada cikin rikicin na jin kai sakamakon takunkumin da Amurka ta sanya kan man kasar. An gudanar da taron koli na kasashen ne domin kare dimukuradiyya da ke fuskantar kalubale daga masu tsattsaurar ra'ayi.
Karin bayani: Ina ganin zan karbe iko da kasar Cuba - Trump
A cikin sanarwar hadin gwiwa da suka fitar, kasashen sun bukaci da a gudanar da zama na musamman tare da neman dakile duk wani yunkuri na mamayar sojoji a Cuban. Shugaba Trump ya sha yin barazanar kaddamar da mamaya a Cuba, kuma kasar ta sha fama da daukewar wutar lantarki sakamakon takunkumin na Amurka.