1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soro ya lashi takobin tsayawa takara

Mouhamadou Awal Balarabe
September 17, 2020

Kwanaki kalilan bayan da kotun tsarin mulkin côte d' Ivoire ta yi watsi da takararsa, dan adawa Guillaume Soro ya ce zai ci gaba da takarar shugabancin kasar na watan Oktoba ko ana ha-maza ha-mata.

https://p.dw.com/p/3icNd
Elfenbeinküste Guillaume Soro Gründung Partei Political Committee
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Tsohon shugaban ‘yan tawaye kuma tsohon firayiministan Côte d'Ivoire Guillaume Soro ya jadadda aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasa ta ko halin kaka, duk da watsi da takardunsa da kotun tsarin mulkinsa kasar ta yi. A yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Paris, tsohon kakakin majalisar dokokin Côte d' IIvoire ya yi kira ga 'yan adawa da su hada kai don neman kungiyar ECOWAS ko CEDEAO ta tabbatar da cewa an dama da kowa da kowa kuma an gudanar da sahihin zabe.

Soro ya nemi a dage zaben shugaban kasa da ya kamata ya gudana a ranar 31 ga watan Oktoba idan ana so a maagance abin da ya kira juyin mulki da shugaba Ouattara ke shirin aiwatarwa. Dama dai a ranar Talata, kotun kare 'yancin bil Adama ta Afirka, wacce hukumomin Abidjan suka nisanta kansu da ita, ta nemi Côte d'Ivoire da ta ba wa Guillaume Soro damar tsayawa takarar shugaban kasa.

kotun tsarin mulki ta tabbatar da takarar Shugaba Alassane Ouattara tare da kin amincewa da takarar abokan hamayyarsa tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo da kuma Guillaume Soro, wadanda ke zaman gudun hijira a Faransa.