Soraz matatar mai ce da ke Nijar wadda kamfanin mai na China ya gina a jihar Damagaram da ke Nijar din.
Matatar man ta fara aiki ne lokacin shugaban mulkin sojan kasar Saliou Djibo a shekarar 2011. Matatar man na fidda ganga dubu 20 a kowacce rana, wanda 'yan kasar ke amfani da ganga dubu 7 daga cikin wannan adadi.