Somaliya na neman tallafin kasashen Duniya | Labarai | DW | 11.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Somaliya na neman tallafin kasashen Duniya

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, tare da Firaiministan Birtaniya Theresa May sun bukaci hadin guiwa daga kungiyoyin kasa da kasa da nufin rage matsalar fari da ke addabar Somaliya.

Makasudin taron shi ne nazarin hanyoyin kulla sabuwar huldar kasashen duniya da Somaliya, a fannin harakokin tsaro da tattalin arziki da zimmar taimakawa kasar ci gaba kamin shekara ta 2020. Taron ya hada kan kungiyoyi kimanin 40 da suka hada da Bankin Duniya da kuma Kungiyar tarayyar kasashen larabawa.

Majalisar Dinkin Duniya na bukatar kimanin kudi da ya kai dala miliyan 900 a wannan shekara, da za'a tallafawa kasashen Afirka da ke cikin matsin rashin abin da tabarbarewar tsaro. A yanzu an yi kiyasin mutane miliyan shida ke fuskatantar barazanar yunwa a kasashen Afirka, yayinda matsalar fari ya yi sanadiyar raba daruruwar 'yan Somaliya da muhallansu tun bayan barkewar matsalar a watan Nowamba shekara ta 2016.