Somaliya: Fari na barazanar yunwa ga dubban mutane | Labarai | DW | 20.12.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Somaliya: Fari na barazanar yunwa ga dubban mutane

Akalla mutum daya cikin hudu na fuskantar barazanar yunwa a Somaliya a sabili da fari da kasar ke fuskanta a cewar Majalisar Dinkin Duniya a wani rahoton gargadi da ta fidda a yau.

Flash-Galerie Somalia Flüchtlingslager in Mogadishu

Wannan dai na zuwa ne bayan karancin ruwan saman da kasar da ke fama da rikicin ta'addanci ta fuskanta na kusan damina hudu a jere. A cewar rahoton matsalar za ta yi kamarin da za ta kai ga barin kusan mutum miliyan 5 ga bukatar agajin gagawa na abinci.

Sama da shekaru 30 Somaliyar bata taba fuskantar irin wannan hali na fari da ta shiga ba. A cewar jami'in hukumar tallafin abinci Adam Abdelmoula, kananan yara daga shekaru biyar zuwa kasa wajen dubu 300 ke cikin hadarin fuskantar karancin abinci mai gina jiki cikin watanni masu gabatowa..

A watan da ya gabata ne mahukunta a Somaliya suka ayyana wannan matsala ta fari a matsayin agaji na gagawa.