Somaliya: Dan siyasa ya kai harin bam | Labarai | DW | 27.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Somaliya: Dan siyasa ya kai harin bam

Wani tsohon dan majalisar dokokin Somaliya ya na cikin mutane biyu da suka kai harin kunar bakin wake a birnin Mogadishu fadar gwamnatin kasar.

Tsohon dan majalisar dokokin Somaliya ya na cikin mutane biyu da suka kai harin kunar bakin wake kan dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen duniya kusa da filin jiragen sama na Mogadishu babban birnin kasar a wannan Talata da ta gabata. A cikin wata sanarwa kungiyar al-Shabaab mai kaifin kishin addinin Islama ta ce Salah Nuh Ismail wanda ake kira Salah Badbado tare da wani suka kai harin.

A shekara ta 2010 tsohon dan majalisar ya fice daga cikin gwamnati ya koma bangaren tsagerun, bayan shafe kimanin shekaru 10 a majalisar dokoki. Tsohon dan majalisar da wani sun kai harin a wajen da ake binciken ababen hawa, lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama. Tarayyar Afirka gami da Majalisar Dinkin Duniya sun yi tir da harin sannan suka ce jami'ansu ba sa cikin wadanda harin ya ritsa da su. Somaliya ta shafe shekaru da dama cikin rikici.