Soke musayar kudaden waje a Najeriya | Siyasa | DW | 13.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Soke musayar kudaden waje a Najeriya

Matakin da babban bankin Najeria ya dauka na dakatar da bayar da kudaden kasashen waje ga kamfanonin musayar kudi na ci gaba da jawo kace-nace a tsakanin alumma.

Dubban mutane ne dai suka dogaro da harkar chanji domin samar wa kansu abin yi wanda hakan kuma ke basu damar samun na sakawa a bakin salati. Sai dai wasu masana na ganin cewar dama tun wuri ya dace a dauki matakin, duba da hadarin da yake da shi ga tattalin arzikin kasar, yayin da su kuma masu chanji ke kukan cewa an raba su da hanyar neman abinci.

Makomar hada-hadar kasuwanci a Najeria

Masana tattalin arziki dai sun sanar cewa daukan wannan mataki da babban bakin ya yi shi ne daidai, musamman idan aka yi la'akari da yadda galibi yan chanjin ke mayar da sana'ar wata hanyar arzurta kansu cikin kankanin lokaci. gwamnatin dai na bayar da dalar Amirka ga kamfanonin chanji da ake cewa BDC sau biyu a ko wane mako da nufin rage radadin samun dalar ga alumma. Sai dai kuma yawancin masana na cewa ba kasafai yan chanjin ke amfani da dalar ta hanyar da ya dace ba.

Docta muktar Aliyu Shehu masanin tattalin arziki ne kuma malami a sashen kasuwanci na jami'ar northwest da ke Kano, ya ce matakin ya zo dai dai lokacin da ya dace amma fa yana da matsala waje guda kuma yana da nasa alfanu.

'Yan kasuwan canji sun koka

To amma wanan mataki ya jefa 'yan kasuwar chanji cikin wani yanayi na fargaba lamarin da yasa suke cigaba da bayyana takaicinsu bisa wannan mataki na gwamnati wanda suka ce bata yi shawara ba kafin zartas dashi. To sai dai kuma yayin da su yan kasuwar ta chanji da ma wasu mutanen ke ganin cewar wannan mataki zai zama barazana shikuwa Malam Abubakar Saddik mai fashin baki kan tattalin arziki ya ce babu wata barazana.

Yanzu haka dai kungiyar yan chanji ta Arewa maso Yammacin Nigeria ce ke cigaba da rokon gwamnati kan ta sauya shawara, inda suka ce su masu bin doka da oda ne kuma gwamnati ta sauya tunani. Yanzu haka dai farashin dala a kasuwar chanji ya kara tashi matuka sai dai amsana na cewar tashin ba zai dore ba, kuma tun dama haka farashi yake, yana hawa yana sauka.

Sauti da bidiyo akan labarin