Soke fara shuka irin zamani a Ghana | Zamantakewa | DW | 11.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Soke fara shuka irin zamani a Ghana

An samu cece-kuce a Ghana dangane da shigo da wani sabon nau'in irin shinkafa da kuma wake na zamani da ake son fara shukawa, wanda ya sami amincewar gwamnatin kasar.

Mata na aikin gona a Ghana

Mata na aikin gona a Ghana

Gwamnatin dai ta amince da soma gwajin irin zamani sai dai lamarin ya fusaknci cikas biyo bayan umurnin da wata babbar kotun birnin Accran Ghana ta bayar na dakatar da samar da irin wake da shinkafar wadanda aka sauya fasalinsu a kimiyyance.

Gonaki a nahiyar Afirka yayin shuka

Gonaki a nahiyar Afirka yayin shuka

Hadari ga lafiyar al'umma

Wata kungiya mai suna Food Sovereignty Ghana FSG ce dai ta kai batun gaban kotun inda ta yi zargin cewa nau'in irin na wake da shinkafar na da hadarin da lafiyar al'ummar da za su yi amfani da su a kasar, lamarin da kotun ta ce ta saurare shi kuma sai an kammala bincike a dokance.

Barazana ga manoma

Mace na yin shikar hatsi a Ghana

Mace na yin shikar hatsi a Ghana

Suma manoman kasar Ghanan a daya hannu sun nuna goyon bayansu ga matsayin wannan kungiya ta FSG inda suka ce idan har aka kyale wannan sabon abinci ya shiga kasuwa, lallai yana iya zama barazana a gare su, don ba mamaki ya iya shafar abincin gargajiya da su ke nomawa. Sai dai masana kimiyyar kasar na ganin cewa an dai hurewa al'umma kunnuwansu ne ta hanyar tsoratar da su cewa irin na zamani yana da illa kawai, domin su nuna adawarsu da shi.

Sauti da bidiyo akan labarin