1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: 'Yan ta'adda sun kashe sojoji

Abdoulaye Mamane Amadou
December 24, 2020

Jami'an tsaron Nijar sun halaka a wani harin ta'addancin a yankin Tillaberi da ke yammacin kasar, a yayin da sojojin kasar su kuma suka kashe mayakan jihadi 11.

https://p.dw.com/p/3nC8u
Niger Armee
Hoto: picture-alliance/Zuma/Planet Pix/A.F. Echols

Ma'aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta sanar da mutuwar sojojin kasar bakwai a yayin wani kwantar baunar 'yan ta'adda a kauyen Tarun da ke arewacin Ouallam.

Sai dai sanawar da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar, ta ce rundunar zaratan sojanta, ta samu nasarar hallaka mayakan jihadi 11 a yayin batakashin da 'yan ta'adda, da ya gudana a ranar Litinin a yankin Tillaberi mai fama da hare-haren kungiyar da ke da'awar jihadi.