Sojojin Najeriya sun yi ikirarin kashe ′ya′yan Boko Haram 150 | Labarai | DW | 18.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Najeriya sun yi ikirarin kashe 'ya'yan Boko Haram 150

Wannan labari da ya fito a wannan Laraba ya ci karo da ikirarin da Boko Haram ita ma ta yi cewa ta kashe sojoji 40 a wani kwantan bauna da ta yi wa rundunar ta Najeriya.

Rundunar sojin Najeriya ta fada a wannan Laraba cewa wani farmaki da sojojin kasar suka kai makon da ya gabata a kan wani sansanin Kungiyar nan da ake wa lakabi da Boko Haram, da ke arewa maso gabacin kasar ya yi sanadiyar mutuwar 'yan bindigar Islama 150 da sojoji 16. Sai dai wasu rahotanni sun ce sojoji 40 suka mutu a wani kwatan bauna da 'ya'yan Boko Haram suka yi wa wani gungun sojoji sannan wasu da dama sun bata. Sai dai babu wani jami'in sojin da ya yi karin bayani game da rahoton da ke cewa Boko Haram ta yi musu kwantan bauna, in ban da farmakin da rundunar ta ce ta kai a makon da ya gabata, wanda sai a wannan Laraba labarin ya fito fili. An jiyo kakakin soji Ibrahim Attahiru na cewa sansanin na 'yan kutse da ke cikin dajin Kasiya a jihar Borno na da girma kuma sun gano manyan makamai a ciki.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu