Sojojin Najeriya sun kashe 'yan Boko Haram
September 7, 2013Talla
Wani kakakin rundunar, Sagir Musa a garin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno ya shaida wa 'yan jaridu cewar, sojojin sun kai farmakin ne, ga maɓoya ta ƙarshe inda 'yan ƙungiyar suka ja da'ga a jihar ta Borno da ke zama cibiyarsu.
A ranar Alhamis da ta gabata (05. 09. 13), wasu mutane ɗauke da makamai waɗanda aka ce mayaƙan ƙungiyar ne ta Boko Haram sun kashe mutane guda15 a sa'ilin da suka buɗe wuta a cikin wata kasuwa da ke a garin Gajiram a yankin arewaci na ƙasar. Rundunar ta ce ' yan ƙungiyar na kai hare-haren ne na ɗaukar fansa a kan farar hula a yankin arewa maso gabashi na ƙasar.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh