Sojojin Najeriya sun kashe Abubakar Shekau | Labarai | DW | 24.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sojojin Najeriya sun kashe Abubakar Shekau

A karon farko rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da hallaka jagoran Boko Haram Abubakar Shekau.

Rundunar ta sanar da cewar sojojin sun samun gawar mutumin da ke zaman jagoran masu tada ƙayar bayan.Kakakin sojin Najeriyar Manjo Janar Chris Olukolade ya shaida wa manema labarai a birnin Abuja cewar,An kashe Mohammed Bashir yayin fafatawar da aka yi a garin Konduga na Jihar Borno da ke a yanki arewa maso gabashin ƙasar.

Kuma ya ce shi ne yake fitowa a faifan bidiyo a matsayin jagoran ƙungiyar,wato Abubakar Shekau wanda aka daɗe da kashewa.